9 Maris 2015 - 10:51
Sojojin Iraki na samun nasara akan Da'ish

Yau kwanaki takwas kenan da fara yunkurin 'yanto yankin Salahuddin daga hannun 'yan ta'adda na Da'ish, wanda sojoji da hadin kan mutanen Iraki suka soma, ya zuwa yanzu an 'yanta garuruwa da dama kuma nan da lokaci kadan za'a kwato Takrit

Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna-kwamandan dake jagorantar yanto yankunan da 'yan ta'adda suka mamaye yace, kama yanzu mun kewaye garin Takrit ta bangarori hudu,  Janar Abdulwahab ya kara da cewa, mun yaudari 'yan ta'adda ta inda muka fara kai masu hare-hare ta sama a inda sukayi dan-dazo sannan muka tura sojojin mu ta kasa da nufin 'yanto Takrit amma nufin mu shine 'yanto sauran yankunan Salahuddin.

Kwamandan ya yabi cigaban da sojin kasar ke samu tare da hadin gwiwar sojin sa kai wajan yakar 'yan ta'adda na Da'ish.ABNA