Dokar ta kuma kara bai wa al’ummar Musulmin kasar ‘yancin gudanar da addininsu ba tare da wata tsangwama ba.
Sai dai dokar ta gamu da suka daga sassa dabam dabam, cikin su har da Musulmin kasar da ke shirin kalubalantar dokar a kotu.
Ko a watan jiya shugaban Amurka Barack Obama ya bukaci janyo al’ummar Musulmi a jika maimakon yadda ake nuna musu kyama.ABNA