An sako Gamal da Alaa Mubarak ne da safiyar ranar Litinin.
An kama su ne tare da mahaifinsu bayan an hambarar da Mista Mubarak a farkon shekarar 2011 sakamakon bore na makonni da ake yi na kin jinin mulkinsa.
An tuhume su ne da cin hanci da rashawa, kodayake a makon jiya kotun ta bayar da umarnin sakin su har sai an sake yin shari'a game da batun.
Mista Mubarak na ci gaba da kasancewa a wani asibitin sojin kasar, inda yake a daure bayan an same shi da laifin almubazzaranci da dukiyar kasa.ABNA