Wadanda suka shaida lamarin sun ce mayakan na Boko Haram sun shiga birnin na Damaturu ne bayan faduwar rana a jiyan.
Bayan shigar ta su ne wasu mazauna birnin suka ce aka shiga musayar wuta tsakaninsu da sojoji.
Wannan dai shine hari na biyu da a baya-bayan nan 'yan Boko Haram din suka kai a birnin na Damaturu.
A farkon watan jiya ma sun yi wani yukuri na kame birnin, amma sojojin suka fatattake su.ABNA