27 Disamba 2014 - 08:12
Shahadar shugaban ofishin Ahlulbait{a.s} dake uganda

Shugaban ofishin mu'assa na Ahlulbai{a.s}dake uganda yayi shahada daren juma'a bayan ya fito daga taron adu'a inda wasu mahara sukayi kai masa hari wanda hakan ye sanadiyar shahadarsa.

Taskar labarai ta Ahlulbait{a.s}-abna- ta rawaito cewe; daren juma'a wasu yan ta'adda sun kaima shugaban ofishin mu'assa ta Ahlulbai{a.s} dake uganda hari wanda hakan ye sanadiyar shahadarsa.

Shahidin mai suna shaikh Abdulgadir ya hadu da shahadar ne jim kadan bayan ya fito daga taron karatun adu'a{du'al khumail}inda wasu mutane masu dauke da makami wadanda ba asan suba suka kai masa hari  wanda haka yai sanadiyar shahadar sa.

Jiya juma'a ne aka dauki kawar mamacin daga kamfala baban birni kasar zuwa garin su inda akai masa jana'za kamar yadda Addinin musulunci ya tanada.

Shaikh Abdulgadir yayi karatun digiri na ukku {daktora} a kasar kenya.Abna