Wata sanarwar da hukumar ta WHO ta fitar a birnin Geneva, ta bayyana cewa, a ranar 20 ga watan nan na Nuwamba, aka cika kwanaki 42 da sallamar mutum na karshe dake dauke da cutar ta Ebola daga asibiti, bayan da aka yi masa gwaji har sau biyu, aka kuma tabbatar ya warke sarai. Bisa sharuddan hukumar WHO dai sai an kwashe kwanaki 42 da samun bullar cutar ta Ebola a karo na karshe, za a iya tabbatar da rashin cutar baki daya. Hukumar WHO dai ta jinjinawa mahukuntan kasar ta Congo, bisa kokarin dakile yaduwar wannan cuta, da kuma irin goyon baya da suka baiwa sassa daban daban wajen wannan aiki, ABNA
24 Nuwamba 2014 - 11:03
Lambar labari: 653630
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar da cewa, yanzu haka babu sauran mutane dake dauke da kwayar cutar Ebola a kasar Congo (Kinshasa), sakamakon nasarar yakin da aka yi da cutar