Tashar television na Presstv mai yada shirye shiryensa da harshen turanci a nan Tehran ya nakalto Abbass Iraqchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kuma jiko a tattaunawan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take yi da kasahen yamma kan shirin ta na makamashin nuclear yana cewa tattaunawar ta yi armashi amma babu wata matsaya guda da bangarorin ukku suka cimma ya zuwa yanzu.
A jiya litinin ne ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Zarif, da sakataren harkokin wajen kasar Amurca John Kerry da kuma Katrina Ashton jami’ar harkokin wajen tarayyar turai mai baring ado suka kammala taron kwanaki biyu a birnin Muscat na kasar Omman.
Bangarorin biyu dai suna kokarin ganin sun cimma matsaya guda kafin ranar 24 ga watan nwamba lokacinda wa’adin tattaunawan zai kawo karshe. ABNA