11 Nuwamba 2014 - 15:08
Hukumar Zabe A Sudan Ta Kara Lokacin Yin Rajistan Sunayen Masu Zabe A Kasar

Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar Sudan ta sanar da karin lokacin yin rijistan sunayen mutanen da suka cancanci kada kuri'a a lokutan zabuka a kasar.

 

A jawabinsa ga manema labarai a yammacin jiya Litinin; Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar Sudan Mukhtar Asam ya bayyana cewa manufar kara yawan kwanakin yin rajistan sunayen mutanen da suka cancanci kada kuri'a ita ce domin al'ummar Sudan su samu damar yin rajistan sunayensu.

Har ila yau shugaban Hukumar zaben a Sudan ya bukaci dukkanin jam'iyyun siyasar kasar da su dauki matakin kwadaitar da magoya bayansu kan hanzarta yin rajistan sunayensu.

A yau Talata ne wa'adin da aka gindaya na yin rajistan sunayen mutanen da suka cancanci kada kuri'a a Sudan zai kawo karshe, amma hukumar zaben ta kara tsawon kwanaki hudu, wato zuwa ranar 15 ga wannan wata na Nuwamba. ABNA