Kamfanin dillancin labaran Reuters ya watsa rahoton cewa: ‘Yan adawa a Equatorial Guinea sun kaurace wa zaman taron kasa da gwamnatin kasar ta shirya a jiya Lahadi sakamakon matakin da gwamnatin ta dauka na kin cika alkawarin da ta dauka musu na sakin fursunonin siyasa.
A nata bangaren tawagar gwamnatin kasar ta Equatorial Guinea a zaman taron na kasa ta zargi ‘yan adawan da kokarin yin yankar baya ga dokokin kasa ta hanyar neman sakin masu laifi da ake tsare da su a gidan kurkuku da sunan ‘yan siyasa, tana mai da’awar cewa babu wani dan siyasa da ya rage a tsare a gidan kurkukun kasar. ABNA