4 Nuwamba 2014 - 07:27
Libya : An Dage Sauraron Shari'ar Jami'ai Sofuwar Gwamnatin Ghaddafi Har Zuwa Ranar 16 Ga Wata

Wata kotu a Libya ta dage sauraron shari'ar jami'ai sofuwar gwamnatin tsohon shugaban kasar mirigayi Mu'ammar Ghaddafi zuwa ranar16 ga watan nan na Nowamba da muke ciki.

 Shari'ar ta jami'ai 23 da aka tsara yi a ranar lahadin data wuce ana yin ta ne a gidan yarin al-Hadba dake birnin Tripoli, sai dai ganin wanda ake zargi na farko Saif Al-Ghaddafi bai bayyana a lokacin shari'ar ba bisa ga jinkirin dauko shi sabilin masalar na'urar bude kofofin gidan yarin Zintan inda yake tsare. don haka mai shari'ar a lokacin bayan shawarwari da sauran alkalai ya dage sauraron karar zuwa 16 ga watan Nuwamba. Su dai wadanda ake zargin, ana tuhumar su ne da laifuffuka da dama da suka hada da laifin mara wa tsohuwar gwamnati Ghadafi baya, abin da ya janyo boren shekara ta 2011, cin hanci da rashawa da kudaden gwamnati, kisan kare dangi da fyade. ABNA