3 Nuwamba 2014 - 06:38

Rundunar sojin kasar Libya da ke biyayya ga janar Khalifa Haftar ta bukaci mazauana yankunan da ke gabar ruwa a birnin Benghzi, a shirin da sojojin suke yin a kaddamar da wani gagarumin farmaki a kan wadannan yankuna domin murkushe 'yan bindiga.

Kakakin rundunar sojin Ahmad Mismari ya fadi a yammacin jiya cewa, suna kiran fararen hula da su janye daga wadannan yankuna, domin kuwa masu dauke da makamai da ake da alaka da alikaida ne suke  iko da wannan yankuna da suka kunshi tashar jiragen ruwa mafi girma a Benghazi. Fiye da mutane 230 ne suka rasa rayukansu a cikin makonni biyu a Benghazi,  a ba-ta-kashin da ake yi tsakanin dakarun na Libya da kuma tsoffin yan tawayen kasar da suka kashe marigayi Ghaddafi.

 

A nata bangaren gwamnatin Libya, a jiya Lahadi ta zargi kasar Qatar da mara baya ga 'yan tawayen, inda  acikin wannan mako wani babban jirgin daukar kaya (cargo) ya safaka a filin safka da tashin jiragen sama na birnin Misrata wanda ke hannun 'yan tawayen, inda jirgin ya safke muggan makamai a wurin, bayanin gwamnatin Libya ya ce wannan shi ne karo na biyar da jirgin na gwamnatin Qatar yake safke muggan makamai ga 'yan tawayen a garin Misrata a cikin 'yan lokutan nan. ABNA