Har ila yau hukumar lafiyar ta bayyana cewa yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar Ebola sun kai kashi 70 cikin dari a kasashen 3 da cutar ta bulla a cikinsu dake yankin yammacin Afrika, kamar yadda Bruce Aylward, mataimakin darakatan hukumar lafiya ta Majalisar DD Ya sanar a jiya talata
Yanzu haka dai za a iya cewa cutar ta Ebola ta kusa zama annobar daukacin kasashen duniya sakamakon mutuwar wani jami’in Majalisar DD da ya kamu da cutar, bayan kwantar da shi a wani asibiti dake kasar Jamus a jiya talata, yan sa’oi bayan soma gudanar da zaman taron kwamitin tsaro na MDD, kan yaki da cutar ta Ebola, wace ta yi sanadiyar mutuwar sama da mutane dubu 4 a yankin yammacin Afrika.ABNA