Shafin watsa labaran World Tribune na kasar Amurka ya bada labarin cewar wata majiyar jakadanci ta tabbatar da cewa: Mahukuntan Saudiyyya sun karbi bakoncin wasu dubban ‘yan ta’adda kimanin 5,000 da suka fito daga kasashen Siriya, Turkiyya da wasu kasashen da suke yankin gabas ta tsakiya domin horas da su dabarun yaki da nufin aikewa da su zuwa kasar Siriya don kifar da gwamnatin Bashar Asad tare da murkushe ‘yan kungiyar Da’ish, kuma za a dauki tsawon watanni hudu zuwa shida ana bada horo ga gungun ‘yan ta’addan.
Majiyar ta kara da cewar shirin mahukuntan kasar ta Saudiyya na horas da gungun ‘yan ta’addan kasa da kasa da yawansu zai kai 15,000 ya samu cikakken goyon bayan gwamnatin Amurka, kuma shine a maimakon rawar da Saudiyya zata taka a fagen yaki da kungiyar ta’addanci ta daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish. ABNA