30 Satumba 2014 - 11:19

Gwamnatin kasar Tunisia ta sanar da kafa wata cibiya ta musamman da za ta sanya ido kan 'yan ta'addan kasar da suke yaki a Syria a cikin sahun kungiyoyin 'yan ta'adda na kasashen duniya da suke da gwamnatin kasar ta Syria da sunan jihadi.

Jaridar Al-musawwir da a ke bugawa a birnin Tunis ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar ta Tunisia ta dora alhakin kafa wannan cibiya ne a kan hukumar tsaron cikin gida, wadda za ta rika bin kadun dukkanin abubuwan da suke faruwa tare da tattara bayanai kan 'yan kasar Tunisia wadanda adadinsu ya haura 6000 da suke yaki tare da 'yan ta'adda a Syria.

 

Gwamnatin Tunisia ta dauki wanann mataki ne domin yin aiki da kudirin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, wanda ya tilasta wa kasashe da su dauki matakai kan 'yan kasashensu da suke zuwa Syria ko Iraki domin jihadi. Kasar Tunisia dai ta kasance daga cikin kasashen da suka bar kofa bude ga 'yan ta'adda domin zuwa Syria, kafin daga bisani kasar ta dauki matakin hana yin hakan. ABNA