Har ila yau ana sa ran a safiyar ta yau, shugaba Rauhani zai gana da Piraministan Japan, shugabanin kasashen Turkiya, Faransa da kuma Osteriya.
A marecen yau kuwa, a na sa ran shugaban kasar ta Iran zai gana da babban saktaren Majalisar dinkin duniya Banki Moon bayan haka ya halarci tashar telbijin ta Ebay domin amsa tanbayoyi.
Har ila yau rahoton ya ce bulaguron na shugaban Rauhani zai kai har yammacin Assabar a birnin na News York inda zai gabatar da jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 69 tare da ganawa da wasu jami'an kasashen duniya gami da amsa tambayoyin manema labarai.
A bangare guda tun ranar Talatar da ta gabata ce, Ministan harakokin wajen jasar Iran Muhamad Jawad Zarif ke birnin na News York inda ya ke jagorantar tawaggar kasar Iran dangane da tattaunawar da a ke yi tsakaninsu da manyan kasashe biyar masu kujerar din din-din a majalisar dinkin duniya da kuma kasar Jamus dangane da shirin nukiyar Iran na zaman Lahiya. abna