17 Satumba 2014 - 15:28
Yan Tawayen Sudan Kimanin 2000 Sun Mika Makamansu Ga Gwamnatin Kasar

Yan tawayen Sudan kimanin 2000 ne suka ajiye makamai tare da mika kansu ga rundunar sojin gwamnatin kasar.

Shafin watsa labaran Sudan na “Safari” a yau Laraba ya watsa rahoton cewa; ‘Yan tawayen Sudan 1,900 ne da suke dauke da makamai a lardin Kordofan ta Kudu da ke kudancin kasar suka dauki matakin ajiye makaman tare da mika kansu ga rundunar sojin gwamnatin kasar.

A taron manema labarai  da jagoran tawagar ‘yan tawayen ya gudanar mai suna Abdullahi Qasmullahi ya yi furuci da cewar sun cimma shawarar ajiye makamai ne shi da tawagarsa da nufin shiga cikin shirin gwamnatin Sudan na gina kasa, kuma babu wani taimako da yaki zai yi wajen warware rikici a duk wata kasa banda kara rusa wannan kasar. ABNA