A cikin wasikar shugaba Rauhani ya nuna cikakken goyon bayansa ga sabuwa gwamnatin ta kasar Iraki, tare da yin fatan kasar ta samu kwanciyar hankali da zaman lafiya, ya kara da cewa Iran za ta ci gaba da taimaka ma Iraki a dukkanin bangarori domin ganin kasar ta tsaya da kafafunta.
A daren jiya ne dai majalisar dokokin kasar Iraki ta amince da sabuwar gwamnatin kasar karkashin jagorancin Haidar Ibadi, wannn dai ita ce gwamnati ta biyar da aka kafa a kasar Iraki tun bayan hambarar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Saddam Hussai a cikin shekara ta 2003, wanda manyan aminansa Amurka da kasashen turai suka hambarar da shi. ABNA