A jawabinsa da ya gabatar a jiya Litinin; Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrof ya bayyana cewar gwamnatin Rasha tana goyon bayan yakin da gwamnatin Iraki take yi da ‘yan ta’addan kungiyar Da’ish, kuma tana kira ga kasashen yammacin Turai da Amurka su zage dantse a fagen yaki da kungiyar ta Da’ish a dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya ciki har da kasar Siriya.
Lavrof ya kara da cewa; Kasar Rasha tana goyon bayan gwamnatin Iraki a yakin da ta daura da ‘yan ta’adda, kuma zata wadata Iraki da dukkanin makaman da suka dace wajen fada da ayyukan ta’addanci a cikin kasarta.
Wannan jawabi na ministan harkokin wajen kasar Rasha ya zo ne a matsayin mai da martani ga gwamnatin Amurka da wasu kawayenta na kasashen yammacin Turai da suke magana kan hatsarin kungiyar ta’addanci ta daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish a cikin kasar Iraki alhalin suke goyon bayan ayyukan ta’addancin kungiyar a kasar Siriya. ABNA