Har’ila yau a wani labarin kuma gwamnatin HKI ta bada labarin bacewar wani sojanta guda a yankin na Gaza da kuma mutuwar wasu da dama a fafatawarta da dakarun Palasdinawa a Gaza.
Dangane da tattaunawar tsagaita bude wuta kuma, mai magana da yawun kungiyar Hamas Sami Abu-Zuhra ya bayyana cewa dakaru masu gwagwarmaya a yankin Gaza sun mika sharuddunsu na tsagaita bude wuta ga dukkanin bangarorin da abin ya shafa, sannan dukkan bangaroron suna tattaunawa duk samarda da tawaga guda wacce zata wakilcesu a birnin Alkahira don tattauna kan tsagaita bude wuta a gobe Asabar.
Kungiyar Hamas dai ta shardanta bude kofofin shiga yankin gaza wadanda ake rufe fiye da shekaru 8 kafin a yi maganar tsagaita bude wuta tsakaninta da HKI. ABNA