28 Yuli 2014 - 16:48
Iran Ta Bukaci Da A Gurfanar Da Isra'ila A Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad jawad Zarif ya gudanar da wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho tare da babban sakataren majalsar dinkin duniya Ban Ki Moon dangane da halin da ake ciki A Gaza

A yayin zantawar Muhammad Jawad ya sheda wa Ban Ki Moon cewa ya zama wajibi kan majalisar dinkin duniya da ta taka wa Isra'ila birki dangane da kisan kiyashi da take yi kan fararen hula a Gaza, tare da gurfanar da duk wadanda suke da hannu wajen kisan fararen hular Gaza a gaban kotun manyan laifuka ta duniya. 

Kungiyoyn kare hakikin bil adama na kasa da kasa suna ci gaba da sukar lamirin Isra'ila dangane da yadda take yin amfani da makamai da aka haramta yin amfani da su a duniya wajen kashe fararen hula mata da kananan yara a Gaza. ABNA