Wadanda aka tabbatar da mutuwarsu a harin mafi girma da aka kai a mafakar masu tada kayar bayan. manyan masu fada a ji ne na kungiyar Taliban.
Dubban 'yan Pakistan ne dai suka rasa rayukansu a hare-haren bama-bamai da harbin kan mai uwa da wabi tun lokacin da kungiyar Taliban ta fara kaddamar da hare-harenta akan gwamnatin kasar a shekarar 2007.
A baya dai gwamnatin kasar ta sha kaddamar da hare-hare akan 'yan Taliban din, sai dai a yanzu ta bude kofar tattaunawar sulhu da su.ABNA