Wani dan jarida a Jos, ya shaidawa BBC cewar ya kirga gawarwakin mutane 38 a cikin asibitin Jos, a yayinda ya ce yaga an kawo wasu karin gawarwakin a lokacin da yake barin asibitin.
Rahotanni sun ce an soma zaman dar-dar a birnin, saboda matasa sun harzuka sakamakon tashin bam din.
Fashewar dai ta auku ne da misalin karfe uku na rana, a daidai lokacin da 'yan-kasuwa da sauran jama'a ke hada-hada.
Kawo yanzu jami'an tsaro ba su tabbatar da adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata a harin ba.
Birnin na jos na fuskantar rikice-rikicen addini dana kabilanci.ABNA.