20 Mayu 2014 - 11:18

Ana sa ran Majalisar dattawan Nijeriya za ta ci gaba da muhawara kan bukatar da Shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar na neman kara dokar ta-baci.

Tuni dai alamu ke nuna cewa an samu rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan majalisar, bisa dalilai na bambancin jam'iyyun siyasa da bangaranci.

Majalisar za ta jefa kuri'a kan batun idan bakin 'yan majalisar bai zo daya ba yayin muhawarar.

A makon jiya ne Majalisar Wakilan kasar ta amince da tsawaita dokar da watanni shida, a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.ABNA.