Za a fara gangamin ne da misalin karfe uku na yamma agogon kasar, inda matan za su yi jerin-gwano zuwa majalisar dokoki.
Haka kuma za su je ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro, domin mika wasiku zuwa ga shugaban kasa.
Haka zalika za a yi irin wannan gangamin a wasu jihohin arewacin kasar, ciki har da Kano wadda ta fi kowace jiha yawan al'umma a kasar.
Kwanaki 16 kenan tun da wasu da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne suka sace 'yan makarantar a garin Chibok.ABNA.