28 Afirilu 2014 - 10:30
Hukuncin kisa kan mutane 700 a Masar

Wani Alkali a Masar ya yanke hukuncin kisa kan mutane kusan 700 na kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka haramta ciki hadda--shugaban kungiyar Muhammed Badie.

An yanke wa mutanen hukuncin ne sakamakon rikicin da aka yi a birnin Minya a bara inda mutane suka musu sannan aka raunata 'yan sanda.

An mika shari'ar zuwa babban Mufti na Masar don ya sake nazarin shari'ar kafin ya yanke hukunci na karshe a watan Yuni.

Ita ce kotun da ta amince da hukuncin kisa a kan 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi su kusan 40 a watan da ya gabata.

Sannan kuma aka yanke hukuncin daurin rai-da-rai a kan mutane kusan 500. ABNA.