Yau, ita ce ranar da Iran ta ci gaba da wanzuwa; ba wai kawai ta ci gaba da wanzuwa ba, har ma ta soke hasashe da tsare-tsare da yawa da aka rubuta game da makomarta. Wannan shine batun da tarihi zai rubuta game da ita...
Sabon rahoton Hukumar Makamashi ta Duniya ya nuna cewa yakin da ake kan Iran da tashe-tashen hankula a hanyoyin isar da makamashi, sun jefa duniya cikin wani sabon mataki na rikicin tsaron makamashi; rikicin da a cewar darektan wannan hukuma, shi ne mafi girma a tarihin zamani.
Ministan cikin gida na Kenya, Kipchumba Murkomen, ya bayyana cewa mutane huɗu sun rasa rayukansu a jiya Litinin a zanga-zangar da aka yi a garuruwa da dama na Kenya don adawa da hauhawar farashin man fetur sakamakon yaƙi da Iran, bayan da yajin aikin gama-gari a fannin sufuri na jama'a ya bar matafiya a makale.