15 Nuwamba 2026 - 20:35
Source: ABNA24
Sojojin Saudiyya Sun Janye Daga Kewayen Mashigar Babal-Mandab Mai Mahimmanci

Sojojin da Saudiyya ke marawa baya a Yemen sun ba da labarin janyewarsu daga wurinsu a kewayen yankin Dhubab da mashigar Babal-Mandab.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Sojojin da Saudiyya ke marawa baya a Yemen a yau Lahadi sun ba da labarin gudanar da wani aiki mai suna canza tsari da sake tsarawa a yankin da ke fuskantar mashigar Babal-Mandab mai mahimmanci. An ɗauki wannan matakin ne bayan da sojojin Yemen suka gudanar da wani aiki na killacea wurin da suke.

Janyewar baya na sojojin da ke karkashin Saudiyya daga yankin Babal-Mandab, yana samar da dama wajen ƙara ikon sojojin Yemen kan wannan ƴar ƙaramar mashigar ruwa ta teku.

Mashigar Babal-Mandab tana ɗaya daga cikin muhimman kuma mafi yawan zirga-zirgar hanyoyin ruwa na duniya wajen safarar kaya da kayayyakin kasuwanci, musamman kayayyakin da ke zuwa Turai daga Asiya ta hanyar tashar Suez ta Masar.

Wata majiya ta soji ta gaya wa tashar talabijin ta "Al-Masirah" ta Yemen cewa an kori tarukan da sojojin da ke karkashin Saudiyya daga kewayen yankin Dhubab da mashigar Babal-Mandab. A cewar wannan majiya, wannan janyewar ta faru ne bayan da sojojin Yemen suka masu kofar rago.

Wannan majiya ta ƙara da cewa sojojin da suka janye, sun rasa wurinsu da layukan tallafinsu kuma hakan ya tilasta msu guduwa zuwa birnin Aden bisa hujjar cewa suna da niyyar kare birnin Aden.

Wannan majiya ta soji ta nanata cewa hujjar janyewa daga layukan gaba na fadace-fadace da taken canza tsari da sake tsarawa, yana nuni da girman damuwar sojojin da ke karkashin Saudiyya kan tsoron fadawar su cikin tarkon kisa ko kamawa a hannun sojojin Yemen. Musamman da yake an sojojin Yamen sun masu kofar rago kuma sun rasa iyawarsu ta kiyaye wurarensu.

Wannan majiya a ci gaba da nanata ci gaban tunkarar tarukan da motsin abokan gaba da cewa: sojojin Yemen za su ci gaba da tunkarar fagen daga kan motsin Saudiyya da kayan aikinta da hayarta kuma a lokaci guda, za su dage kan ma'aunin killacewa da killacewa da tsanantawa da tsanantawa.

..............................

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha