29 Yuli 2026 - 18:58
Source: ABNA24
Bidiyo | An Fara Jana'izar Shahidan Hashdush Sha'abi Iraki Cikin Girmamawa

Ana ci gaba da gudanar da taron jana'izar gawarwakin shahidan Dakarun Hashdush Sha'abi, waɗanda suka yi shahada sakamakon harin soji na hadin gwiwa tsakanin Saudiyya da Amurka, tare da halartar dimbin jama'a da shugabannin siyasa da soji.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ana ci gaba da gudanar da taron jana'izar gawarwakin shahidan Dakarun Hashdush Sha'abi, waɗanda suka yi shahada sakamakon harin soji na hadin gwiwa tsakanin Saudiyya da Amurka, tare da halartar dimbin jama'a da shugabannin siyasa da soji.

Wasu rahotannin suna cewa wasu daga cikin dakarun Sifah Quds daga Iran guda biyar sun yi shahada a waɗannan hare-haren

Sannan a sakamakon hare-haren da Amurka da Saudiyya suka kai da sanyin safiyar Laraba kan wata hedkwatar sojojin gwagwarmaya a Iraki, an aike da wasu da suka raunata a wannan lamarin zuwa Iran domin samun jinya.

An kai su zuwa ɗaya daga cikin manyan asibitocin yammacin ƙasar, kuma an fara aikin jinyarsu.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha