Ta'addancin yaƙin na hare-haren bama-bamai da Saudiyya ta kai bisa jagorancin Amurka a Iraqi ya shafi harda masallaci ɗakin bautar Allah, a wanann cin zarafi da ya saba wa dukkan kyawawan dabi'u da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa.
Barnar da ta faru sakamakon harin ta'addanci na dabbanci da Saudiyya da Amurka suka kai kan hedkwatar ayyuka ta Basra na dakarun Hashdush-Sha'abi, hare-haren sun shafi cibiyoyin dakarun a lardunan Bagadaza, Wasit, Ninawa, Basra, Kirkuk, Karbala, da Diyala.
Shahadar mayaƙa aƙalla 20, kuma wasu 32 sun sami raunuka, sakamakon farko ba na ƙarshe ba na hare-haren ta'addancin haɗin gwiwar Amurka da Saudiyya wanda suka kai a sassa daban-daban biranen Iraqi, wanda ya shafi wasu cibiyoyi na hukuma na Hashdush-Sha'abi) a wasu larduna na Iraki.