Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Sa'o'i da suka gabata, an fara babban aikin mayaƙan Musulunci don hukunta sojojin Amurka masu kashe yara, saboda dagula tsaron mashigar Hurmuz da kuma ta'addancin da suka yi a wasu wurare na ƙasarmu masoya.
Rundunar sararin samaniya ta dakarun juyin musulunci, sun mayar da wanna dare baƙin dare ga radars da na’urorin tsaron saman Amurka a yankin, a zagaye na 24 na aikin Nasr 2, da lambar albarka "Ya Ruqayya (A.S)," don share fagen babban aiki na gaba, da kuma kawar da cikas na kai hari daidai, sun lalata wata na’urra tsaro da wata radar ta Amurka a Al-Muharraq na Bahrain gaba daya, kuma sun fitar da su daga aiki, haka kuma sun kai hari na hadin gwiwa da makamai masu linzami da jirage mara matuki a kan wata na’urar tsaron Patriot na Amurka a Al-Rifa'a na Bahrain, kuma sun lalata ta.
Hukunta mai ta'addanci na ci gaba, kuma za a kawo rahotonsa ga ku al'ummar masoya da jarumtaka.
…………………………
Ra'ayinka