Lebanon t
-
Lebanon: Isra’ila Ta Kai Hare-Hare Ta Iska Da Manyan Bindigogi Kan Garuruwa Da Dama
Kudancin Lebanon yana fuskantar jerin hare-haren Isra'ila da suka haɗa da hare-hare ta sama kan Zawtar al-Sharqiyah da Mayfadoun da Al-Qantara, da harbin manyan bindigogi kan gefen Zibqin da Yater da Wadi al-Saluqi, ban da hare-haren sama na tsoratarwa a Taya.
-
Sojojin Isra'ila Sun Kona Gidajen Zama A Al-Tiri, Kudancin Lebanon
Sojojin gwamnatin Isra'ila sun kona gidajen zama a garin Al-Tiri, da ke gundumar Bint Jbeil a kudancin Lebanon.
-
Shekaru 48 Da Bacewa; Tarihin Rayuwa Da Sirrin Bacewar Imam Musa Sadr
Shekaru 48 bayan bacewar Imam Musa Sadr, Sheikh Muhammad Ya'qub, da Abbas Badriddin a Libya, makomarsu har yanzu tana ɗaya daga cikin mafi sarkakiyar shari'o'in siyasa na tarihin zamani na Lebanon. Musa Sadr a Lebanon ba malami ne na Shi'a kawai ba; ya kasance mutum ne na zamantakewa da siyasa wanda ya yi ƙoƙari ya mayar da batun samun yancin kasa ya zama bukata ta yan ƙasa, ya yi ƙoƙari don gyara tsarin kabilanci na Lebanon, ya jaddada zaman tare tsakanin Musulmai da Kiristoci, kuma a lokaci guda tare da faɗaɗa hare-haren sahyoniyya, ya goyi bayan gwagwarmaya a kan mamaya. Tafiyarsa zuwa Libya a watan Agusta na shekara ta 1978, ya kawo ƙarshen kasancewarsa a fili da abokan tafiyarsa; wanda jami'an Libya suka bayar da labarin tafiyarsu zuwa Roma daga kasarsu, daga bayan bincike bai yi daidai da sakamakon binciken Italiya da Lebanon ba.
-
Lebanon: Isra'ila Ta Lalata Rukunin Gidaje 85,000 A Kudancin Lebanon
Isra’ila kimanin rukunin gidaje 85,000 a kudancin Lebanon ta lalata ko kuma ta rushe su gaba ɗaya. Barnar ta kuma shafi gine-ginen tarihi da wuraren da ke cikin jerin abubuwan tarihi na UNESCO.
-
Sojojin Isra'ila Sun Kona Garin Al-Khiyam A Kudancin Lebanon
Majiyoyin Lebanon sun tabbatar da aika-aikar sojojin Isra'ila na keta yarjejeniyar tsagaita wuta, inda suka shiga garin Al-Khiyam a Kudancin Lebanon, da gangan suka kona wasu sassansa.
-
A Lebanon Mutuwa Ba Ta Zama Mafaka Ba; Isra’ila Ta Kai Harin Bama-bamai a Makabartun Kudancin Lebanon
Hare-haren bama-bamai na gwamnatin yahudawa a kudancin Lebanon ba wai kawai sun takaita ga lalata gidaje da hanyoyi da gonaki ba, har ma sun kai hari ga makabartu.
-
Hizbullah Na Lebanon Za Ta Gudanar Da Taron Tunawa Da Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali A Dahieh Beirut
Ƙungiyar Hizbullah ta Lebanon ta sanar da shirya bikin tunawa da jagora shahidin juyin juya halin Musulunci a Dahieh ta kudancin Beirut, kuma ta buƙaci jama'ar Lebanon su halarci wannan bikin da za a gudanar da yammacin ranar Laraba mai zuwa.