9 Yuli 2026 - 18:28
Source: ABNA24
Pakistan: An Kashe Jami'an Tsaro 42 Na Pakistan A Hare-Hare Na Kwanaki Hudu

Mai magana da yawun sojojin Pakistan, a taron manema labarai na jiya, ya sanar da cewa, biyo bayan hare-hare uku na wasu 'yan tawaye a jihar Balochistan cikin kwanaki hudu da suka gabata, an kashe jami'an tsaro 42 da suka hada da 'yan sanda 27, sojoji 11 da fararen hula 4.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Ahmad Sharif Chaudhry, mai magana da yawun sojojin Pakistan, a ranar Alhamis (17 ga Yuli) a taron manema labarai ya sanar da cewa, biyo bayan hare-hare uku na manyan 'yan tawaye a jihar Balochistan cikin kwanaki hudu da suka gabata, an kashe jami'an tsaro 42 da suka hada da 'yan sanda 27, sojoji 11 da fararen hula 4.

Waɗannan hare-haren sun haɗa da kwanton bauna da ƙungiyar 'Yancin Balochistan (BLA) ta yi wa ayarin sojoji kusa da Bela-Winder (inda sojoji 11 suka mutu), harin da aka kai wa ofishin 'yan sanda a Ziarat, da arangama a yankin Hana Orak na Quetta.

Mai magana da yawun sojojin Pakistan ya kira waɗannan hare-haren a matsayin "ta'addanci," kuma ya yi iƙirarin cewa suna samun tallafi da goyon baya da masu tsara su daga waje, musamman Indiya da ƙasar Afganistan,; zargi da Islamabad ke yawan yi.

Chaudhry, tare da kiran gwamnatin Afganistan a matsayin "gwamnatin Taliban ta Afganistan ba haalastacciya ba," ya yi iƙirarin cewa ƙasar Afganistan ta zama mafaka ga ƙungiyoyin ta'addanci, kuma ya buƙaci a ɗauki mataki a kan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

Yana mai jaddada cewa Pakistan ba za ta ƙyale a yi amfani da ƙasar Afganistan a kanta ba, ya kara da cewa sojojin Pakistan a wasu ayyukan ramuwar gayya sun kashe 'yan tawaye 54.

Waɗannan abubuwan suna nuna ƙaruwar tashin hankali a Balochistan, inda ƙungiyoyin 'yan awaren Baloch da Tahrik-e-Taliban Pakistan ke aiki.

Har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin dukkan hare-haren gaba ɗaya, kuma Taliban na Afganistan ba su mayar da martani ga waɗannan maganganun ba.

.....................

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha