Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA -: Cikakken Rubutun Saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Zuwa Al'ummar Iran Game Da Yarjejeniyar Fahimtar Juna Tsakanin Shugabannin Iran da Amurka
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ya ku al'ummar Iran mai kishi da aminci
Kamar yadda kuka sani, an sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin shugaban Iran da Amurka. A kan hanyar zuwa wannan mataki, jami'an da ke da alhakin, da cikakken himma da kyakkyawar niyya, sun yi ƙoƙarce-ƙoƙarce da yawa, kuma ba shakka shugaban Amurka cikin yanayin kasawa, ya yi amfani da kowane irin kayan aiki don faruwar wannan lamari.
Ni, tun asali, ina da wani ra'ayin ne daban, amma saboda alkawarin da shugaban ƙasa mai girma, a matsayinsa na shugaban majalisar koli ta tsaron ƙasa, ya yi mini, daga kansa da sauran mambobi, game da kare hakokin al'ummar Iran da kuma fagen gwagwarmaya, kuma ya bayyana daukar alhakin hakan, ya sa na ba da izinin hakan. Ya kuma bayyana cewa idan bangaren Amurka ya so wuce gona da iri, ba za su yarda da shi ba. Daga wannan lokaci, mu, wato ku al'umma mai daraja da wannan bawa maras kima, muna jiran cikar sharuddan da aka ambata. Amma a bayyane yake cewa tattaunawar da za a yi a nan gaba, ba za’a yi ta da nufi yarda da ra'ayin makiya ba. Muna fatan cewa addu'o'in maigidanmu (Allah ya gaggauta fitowar sa mai daraja) za su kawo nau'ikan taimako da nasarori ga al'ummar Iran mai daraja.
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh
Sayyid Mujtaba Hosseini Khamene'i
28 ga Khordad, shekara ta 1405
..........................
Your Comment