Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: Shugaban Majalisar Shura ta Musulunci a wani sako da ya aika da shi a munasabar shigowar farkon watan Muharram, ya bayyana cewa wannan watan yana tunatar da jarumtaka, sadaukarwa da 'yanci, wanda al'ummar Iran, bisa rikonsu da daga koyarwar Ashura da tafarkin shahidai, za su tsaya tsayin daka a kan zalunci da wuce gona da iri, kuma za su ci gaba da tafarkin daraja da tsayin daka.
Fassarar sakon yazo kamar haka:
Bismillahir Rahmanir Rahim
السَّلامُ عَلَیْکَ یا ثارَ اللَّهِ وَ ابْنَ ثارِهِ وَ الْوِتْرَ الْمَوْتُورَ
Muna yin ta'aziyya da juyayi ga dukkan masoya makarantar Ahlul-Bayt (a.s) a munasabar shigowar watan Muharram ya shigo, wato watan jarumtaka da sadaukarwa, watan da tutar 'yanci da neman adalci ta Husaini ke ci gaba da kasancewa a tsaye.
Muharram na bana yana zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar Iran mai girma da ke cikin bakin ciki, ta shafe wasu kwanaki masu wuya na baƙin ciki, kuma a cikin jarabawa ta tarihi, ta sake nuna wa duniya, tare da dogaro da al'adun Ashura, ruhin tsayin daka da juriyarta. Jarumtar 'ya'yan wannan ƙasa a yaƙe-yaƙe na baya-bayan nan guda biyu da aka kakaba ma ta, da kuma tsayin daka na al'ummar Iran a gaban makiya, yana tunatar da wannan gaskiyar cewa al'ummar da ke da Ashura, ba za ta durƙusa a gaban kowace iko ba.
Shahidai masu daraja na wannan yaƙi, su ne masu ci gaba da tafarkin shahidai na Karbala da yaƙin tsaro mai tsarki na shekaru takwas; mazaje da suka kare daraja, tsaro da 'yancin kai na Iran ta Musulunci da jininsu, kuma suka tabbatar da cewa a al'adun Husaini, shahada ba ƙarshen hanya ba ce, sai dai farkon dawwamar wata manufa ce.
A wannan shekara, yayin da muke tarbar kungiyoyi da majalisosin makokin shugaban shahidai (a.s), muna ganin guraren da wasu masoya suka bari a cikin sahun makoki; waɗanda a shekarun da suka gabata suke fadar "Ya Hussain" a gefenmu, amma a yau su baƙi ne a hadarar karimcin Aba Abdillahil-Hussain (a.s), kuma a gaba gaban su, akwai sunan dawwamammen maɗaukar tutar Musulunci mai girma, Jagoran Juyin Musulunci, Imam Shahid Ayatullah Sayyid Ali Hosseini Khamene'i (Allah ya yarda da shi), shahidi mai daraja wanda ya koya mana yadda zamu zama Husainawa, da yadda zamu rayuwa irinta Husaini da tafiya akan tafarkin Husaini har zuwa karshen rayuwa, kuma ya mika tutar yunkurin Ashura da taken 'yanci da neman gaskiya daga Khomeini mai girma (Allah ya jiƙansa) ga nagartacce wanda ya biyo bayansa, ya bar mu da babban baƙin ciki. Tunawa da shahidai da dukkan masoya na Husaini waɗanda ba sa tare da mu, zai rayu a cikin kowace tutar makoki da kowane hawaye na soyayya, kuma za mu ci gaba kamar yadda jagoran juyin juya hali, Ayatullah Sayyid Mujtaba Hosseini Khamene'i ya faɗa, matuƙar muna da rai, za mu neman fansar jininsu.
Ashura a wurinmu, hanya ce da makaranta don yaƙi da zalunci, kare gaskiya da kiyaye mutuncin ɗan adam. Kamar yadda Imam Hussain (a.s) ya tsaya a kan zalunci, al'ummar Iran suma, da suka yi koyi daga wannan jarumtaka mai girma, za su tsaya a kan wuce gona da iri da neman mamaya na masu girman kai.
Da yardar Allah, kuma tare da dogaro da imani, haɗin kai da juriyar jama'a, kamar yadda muka yi nasara a manyan jarabawar da suka gabata, za mu yi nasara a kan manyan ƙasashen duniya; domin alƙawarin Allah na taimakon gaskiya da tsayin daka.
A farkon wannan watan jini da tayar da yunkuri, muna yin alkawari da shahidai masu daraja, musamman shahidai yaƙin da aka kallafa na baya-bayan nan, cewa za mu ci gaba da tafarkinsu, kuma za mu ci gaba da ɗaga tutar daraja da 'yanci na Husaini. Al'ummar Iran ba za su manta da jininsu mai tsarki na shahidansu da zaluncin da aka yi wa Imam Shahidinsu ba, kuma har zuwa a cimma adalci da nasarar gaskiya a kan ƙarya, za su tsaya tsayin daka a wannan hanya".
……………………
Your Comment