Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: Zaman ana yin sa ne domin nuna Allah-wadai ga makasa jikan ma'aiki. Inda Malamai kan shirya wa'azozi daban-daban har ƴan tamsiliyyah kan shirya kwaikwayo, su misalta irin yadda waƙi'ar ta gudanar da yadda shahadar jikan ma'aiki Imam Hussain (AS) da sahabbansa ta kasance a wasu lokutan ma har sukan nuna yadda bayan waƙi'a karbala rundunar Yazidu ta ci gaba da jan iyalan gidan Manzon Allah (S) cikin sarƙoƙi ƙafafun su babu ko takalma.
Har wa yau, Zaman kan haɗa al'ummar Musulmi maza da mata wanda suka fito daga yankuna daban-daban na cikin garin Zariya da kewaye. Al'umma kan shiga cikin yanayi na juyayi tun daga yanayin shiga, har ma da mu'amalar su ta yau da kullum kan canza daidai da yanayi na juyayi.
Akan samu mawaƙan harkar Musulunci kan amfani da irin basirar su wajen shirya waƙoƙi iri daban-daban na juyayi, wanda kan karantar tare da tunasar da al'umma irin yadda wannan waƙi'a ta karbala ta auku, tare da nuna irin darussan da ya kamata a kwaikwaya tun daga rayuwar al'ummar kufa a wancen lokaci da zuwa sadaukar Imam Hussain (AS) da sahabbansa a filin karbala.
Tun a farkon fara wannan zama, Mawaƙa sun gabatar da waƙen juyayi inda daga bisani Shaikh Abdulhamid Bello wakilin ƴan uwa Musulmi na Da'irar Zariya da kewaye ya jagoranci zaman. Ya gabatar da jawabin Ashura tare da yin tsokaci kan tarihin rayuwar Imam Hussain da kuma darussan da ya kamata al'ummar su kwaikwaya na daga wannan waƙi'a ta karbala.
Shaikh ya fara Jawabinsa ne da ta ya al'ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci. Inda yi ke cewa, " shiga sabuwar shekarar Musulunci abun farin ciki ne don haka ya kamata mu ta ya junanmu murna da ganin Allah ya raya mu, mun ga sabuwar shekara. Sannan kuma ana son mutum ya raya dare da ibadoji, bayan nan kuma ana yin zaman makoki domin a wannan watan ne aka yi waki'ar Karbala. daman tun tuni watan Al-muharram, watan juyayi ne amma waki'ar Karbala ita ta kara bude watan".
"Kafin Manzon Allah (A) ya bar duniya ya ayyana khalifansa a doron ƙasa, kamar yanda an yi bayani a ranar GHADEER duk sahabbai sun yi mubayi'a, Manzon Allah yace bayan sa sai Imam Ali, bayan Ali sai Hassan bayan Hassan sai Imam Hussain. Haka har zuwa Kan Imam Mahdi Manzon Allah yace su ne khalifofin Shi guda 12".
Shaikh ya ƙara da cewa, "da yake gidan duniya gidan jarabawa ce, an jarraba Manzon Allah duk da barazanar kafirai, sahabbai da iyalan gidansa duk ya sadaukar dasu domin tabbatar addini. bayan Manzon Allah kuma sai Imam Ali da sauran Imamai duk sun fuskanci jarabawa".
Daga karshe, Shaikh ya yi tsokaci mai tsawo kan fitan Imam Hussain daga Makkah zuwa Madina tare da iyalansa inda ya ke cewa, "Yazidu yasa a kashe mashi Imam Hussain. da imam ya ga haka sai ya fita a makka saboda Kare harami, ya nufi Kufa anan dai yazidu yasa aka tare masa Imam Hussain (AS) har dai aka kai ga shahadantar da Imam da sahabbansa da kuma iyalan gidan".
Jin kaɗan bayan kammala jawabinsa shehin malamin, ya jagoranci gabatar da sallar Magriba da Issha. Kana kuma daga bisani akan karanta addu'o'i na musamman aka sallami kowa.
Rahoto: Salisu Jibril Khidir
Zaria Media Forum
1 Al-muharram, 1448
16 Yuni, 2026
Your Comment