Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: A jawabinsa, ya bayyana cewa, al'amarin Ashura da tattaki ba sabon abu ba ne a Musulunci, suna da tarihi da asali a cikinsa. Ya ce, tun kafin faruwar waki'ar Ashura, an ba Manzon Rahama (S) labarinta, "sanannen al'amari ne tun ma kafin ya afku." Ya ƙara da cewa, maƙiya na tsorata da irin tasiri da karɓuwar al'amarin Ashura a cikin al'umma, wanda ya sa suke yin yunƙuri daban-daban don ganin sun kawo ƙarshen al'amarin.
Sai dai, ya jaddada cewa, "duk wata barazana ba za ta sa mu daina abin da muke yi ba." Ya ce, abin da suke ji ma tsoro lokacinsa ne ya zo; lokaci ne na fahimtar Ahlul Baiti (AS), da samun ƙarfi da yawaitar mabiya bayan ƙaranci da rauni. Ya ƙara da cewa, nasarar Iran a yau tsayuwarta ne a kan wannan tafarki, wanda shi ne turba ta yakar zalunci da tabbatar da adalci.
Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
………………….
Your Comment