Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Matsayin Susan Rice game da sanya hannun Amurka kan yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad tsakanin Amurka da Iran ya zo daidai da matsayin tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Nikki Haley wadda ta ce muna shirin sakin ɗarurruwan biliyoyin daloli da soke takunkumi da kuma yin alkawarin ba da ƙarin kuɗi.
Nikki Haley ta kara da cewa: Iran za ta yi amfani da waɗannan kuɗaɗen kamar yadda take yi koyaushe, don ƙarfafa burinta na nukiliya da tallafa wa wakilan ƙungiyoyinta a kanmu. Biyan kuɗi don sake gina wata barazana da muka lalata, kuskure ne babba.
...........................
Your Comment