Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) cikin wani jawabisa‚ a shekarun baya kafin waƙi’ar Buhari (L) ya ce: "Har wala yau nakan ga mutane su komai sai an ce musu su yi sannan za su yi‚ har ma sai an yi magana an ce Malam ya ce kaza ne sannan za su yi. Haba jama’a‚ sai an ce maka ka yi abu ne? Kai bakasan ya kamata ba ne? Yanzu misali: Muna jaje‚ mukan sanya baƙin kaya‚ sai an ce maka ka sanya baƙin kaya? Wasu za kaga suna da (Jur’a) sosai‚ mutum ya saka farin kaya ya zo ya zauna a tsakanin masu baƙaƙe‚ ya yi zamansa ya yi mirsisi da idanu‚ wai yana Ashura ne‚ kamar yana cewa duk ku wawaye ne, dole ne sai kun sanya baƙin kaya? Ni farina nake sawa kawai.
'Miye na sai an cewa mutum Malam ya ce ka sa baƙin kaya sannan za ka sa? Kai ai ya kamata ka lura cewa ka fita daban a cikin mutane‚ ba sai an ce maka kasa baƙin kaya ba‚ ya kamata kayi kama da sauran mutane kaima. Ba muce lazim ne a sa baƙin kaya ba‚ amma a ƙalla ya kamata ka ji nauyi. Na taɓa halartar wani taro na bikin zagayowar ranar nasarar juyin juya hali na ƙasar Iran a Lagos shekarun baya cikin tamanoni‚ ina jin ko tamanin da bakwai ne? To shikenan‚ sai ya zama wata Ƴar Jarida ta zo taron‚ kuma ita ba musulma ba ce‚ ta zo da gashin kanta a waje ba murfi, kuma ta zo da ɗan guntun kaya, wanda bai rufe gwiwarta ba‚ to amma sai ta ga matan da ke wurin kowa da doguwar riga da lulluɓi‚ ba ma hijabi ne kammalalle ba, amma dai sun rufe kansu.
"To data zauna cikin su duk sai ta ga ita ce kawai ƙafafunta a waje‚ sai tana jan wannan guntun rigar don ya rufe‚ tana ta fizgarshi‚ ƙar she dai ta roƙi wata ta bata abin da za ta rufe kai‚ ta rufe kanta saboda ta ga ta zama daban‚ ta samu ƙyalle ta rufe kanta‚ ta rinƙa jan rigarta mai siketi ko ya rufe mata gwiwa‚ ya kasa rufewa. ƙarshe dai wata ce ta taimaka mata don ta ga halin da take ciki‚ ta ara mata ɗan zani ta rufe ƙafa. Ka ga ta ga ta fita daban‚ wannan ita ba ma musulma ba ce, kuma Ƴar jarida ce‚ amma tunda taga cikin mata ta fita daban, sai taji kunya tana ƙoƙarin ta yi daidai da su.
"Haka ya kamata mutum ya kasance‚ in kana cikin mutane kowa ya sa baƙin kaya kai naka fari‚ to ya kamata ka ji kunya ai. Muna so ne mutun ya rinƙa yin abin da ya dace da kansa‚ ba sai an zungureka ba. Kamar yadda Amirul Muminin (a.s) yake cewa: Dabba ita ce sai an zungureta‚ mai hankali kuwa hankali ya isa ya nuna masa abin da ya dace. Gani ga wane ya isa ishara ga mai hankali. Wannan faɗin Amirul Muminin (a.s) ne.
Gani ga wane‚ ya ishe ka darasi in kai mutum ne‚ dabbace sai an zungureta. In dabba ta fara cin ciyawar gona, ya za ta yi? Zata taci gaba da cin abinta ne sai an doke ta an ce ba a cin wannan‚ wannan yaɓanya ce‚ sannan za ta zuba a guje‚ in ba haka ba kam in an ƙyale ta shi kenan gonar nan lalatatawa za ta yi‚ ba abin da ya dameta..
—Inji Sheikh Ibraheem Zakzaky [H] cikin wani jawabisa‚ a shekarun baya kafin waƙi’ar Buhari (L).
Sheikh zakzakys gallery
01/Al-Muharram/1448.
16/06/2026
Your Comment