Kamfanin Dillancin Labaran Ƙasa Da Ƙasa Na Ahlul-Baiti (As) – Abna - ya bayar da rahoton cewa: Jaridar New York Times a wani rahoto da ta buga ta nakalto wasu majiyoyi biyu da suka nemi a sakaya sunayensu, ta rubuta: Wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin Amurka nau'in Apache ya fadi a ranar Litinin (18 ga watan Yuni) a kusa da mashigar Hormuz, kuma an ceto ma'aikatansa biyu lafiya.
A cikin rahoton New York Times an ce: Ana ci gaba da binciken wannan lamari, kuma har yanzu ba a san ko wannan jirgin da wuta Iran ne ta saukar da shi ba, ko kuma ya sami matsalar fasaha ne, ko kuma ya fuskanci wata matsala ta daban.
Dangane da wannan rahoton, har yanzu jami'an Amurka ba su tabbatar da wannan lamari a hukumance ba, kuma kakakin fadar White House shi ma bai bayar da wata sanarwa ba game da hakan.
…………….
Your Comment