6 Yuni 2026 - 12:57
Source: ABNA24
Yaumul Ghadeer | Darul Qadiriyya Sun Haskaka Yalwan Bene-Soba Da Bikin Yaumul Ghadir + Hotuna

A Jiya Alhamis 4 ga Yuni, 2026, wanda ya yi daidai da 18 Zul-Hijja 1447H, al'ummar Darul Qadiriyya tare da masoya Ahlul Baiti (A.S.) a garin Yalwan Bene, ƙaramar hukumar Soba ta jihar Kaduna, sun gudanar da gagarumin bikin Yaumul Ghadir, domin tunawa da wannan rana mai daraja a tarihin Musulunci.

An fara taron ne da muzahara cikin tsari da lumana, inda mahalarta suka cika titunan garin da kalaman yabo ga Allah Madaukakin Sarki, tare da bayyana farin cikinsu bisa ni'imar wilayar Amirul Mu’minin Imam Ali (A.S.) da kuma sabunta alƙawarinsu na riko da tafarkin Ahlul Baiti (A.S.).

Da yake jawabi a wajen taron, Malam Sani Aliyu na Darul Qadiriyya ya bayyana Yaumul Ghadir a matsayin wata babbar ni'ima daga Allah, yana mai cewa:

“Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa ni'imar wannan rana mai albarka da kuma sanya mu cikin masu ƙauna da biyayya ga Imam Ali (A.S.).”

Taron ya samu halartar manyan malamai daga mazhabobi da dariku daban-daban, ciki har da Alhaji Garba Jibril daga bangaren Shi'a, Limamin Masallacin Juma'a Malam Zakar Ya'u Isma'il, da sauran malamai daga Darikar Tijjaniyya, lamarin da ya ƙara fito da ruhin haɗin kai da zumunci tsakanin al'ummar Musulmi.

An rufe taron cikin kwanciyar hankali da nasara, tare da halartar jama'a daga sassa daban-daban na al'ummar Musulunci, abin da ya nuna muhimmancin Yaumul Ghadir a zukatan masu kaunar Ahlul Baiti (A.S.).

Daga Salisu A. Dahiru

Zaria Media Forum

Your Comment

You are replying to: .
captcha