Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jaridar Financial Times ta ruwaito: A yayin da duniya ke fuskantar mataki mai hatsarin gaske na tabarbarewar makamashi saboda yaƙin da ake yi wa Iran, kusan ƙasashe 80 sun ɗauki matakan gaggawa don kare tattalin arzikin ƙasashensu.
Masana sun yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da dakatarwa da hana fitar da mai ta mashigar Hurmuz, farashin mai zai sake yin tsallen badahu mai girma da ba a taɓa ganin irinsa ba.
A cewar babban masanin tattalin arziki na kamfanin saka hannun jari na "Aberdeen", ya rubuta: Muna nazari da sharhi kan yanayin da farashin danyen mai na Brent zai kai dala 180 a kowace ganga; abin da zai iya haifar da hauhawar farashi da koma bayan tattalin arziki mai tsanani a ƙasashe daban-daban.
Tun lokacin da aka fara yaƙi da Iran, rumbunan taskace mai a duniya sun ragu da kusan ganga miliyan 380.
Your Comment