10 Mayu 2026 - 10:32
Source: ABNA24
Sheikh Zakzaky: Isar Da Saƙon Addini Ta Halayya Da Aiki Ya Fi Muhimmanci Fiye Da Magana

Sheikh Zakzaky: "A Wannan Zamani, Isar Da Saƙon Addini Wajibi Ne Ga Kowane Musulmi Har Zuwa Lokacin Mutuwarsa."

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya rufe Mu'utamar na Lajnut Tarbiya Wattableeg karo na uku, a ranar Lahadi 15 ga DhulQaada 1447 (03/05/2026), a gidansa da ke Abuja.

A jawabin sa, ya bayyana muhimmancin isar da saƙon addini, wanda ya ce isar da saƙon da na baya su ka yi, shi ya wanzar da addinin zuwa yau, haka ma yanzu, aikin isar da saƙon shi ne abinda ya hau kan kowane musulmi har ƙarshen rayuwarsa, kamar yadda Imam Hussain (A.S), har ƙarshen numfashinsa yana mai wa'azi ga makasansa, ta haka ne za a wanzar da shi ga masu zuwa. A lokaci guda, ya jaddada muhimmancin yin tabligi ta hanyar ayukka nagari, "isar da saƙo ta hanyar aiki shi ya fi muhimmanci fiye da murya."

A ci gaban jawabin, ya ja hankali da cewa, dole ne a fuskanci jarabawa daga mahukunta da masu goya masu baya, kamar yadda ya faru a tsawon tarihi, sai dai, ya yi albishir da cewa, muminai ke nasara a ƙarshen lamari, kamar yadda Allah Ya yi alƙawari. A ƙarshe, ya jaddada muhimmancin yin wa'azi ga mutane ta hikima da kyayakkyawan salo da zai sa su fahimta, ba saɓanin haka ba.

Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

15/DhulQaada/1447

03/05/2026

Your Comment

You are replying to: .
captcha