4 Mayu 2026 - 17:10
Source: Quds
Zane-zanen Fasaha A Tashar Jiragen Ruwan Gaza Don Nuna Goyon Baya Ga Ayarin Samoud

A tashar jiragen ruwa ta Gaza, inda teku ya ke shan fama da matsanancin ƙawanya da wahalhalu cikin shekaru masu yawa, masu fasaha na Falasdinawa sun ƙirƙiri zane-zanen fasaha don nuna goyon bayansu ga tawagar "Jiragen Ruwa na Duniya na Samoud".

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Waɗannan tawagar Jiragen Ruwan sun shirya karya kawanyar da aka yi wa zirin Gaza wanda a hanyar su tun fara motsawarsu Isra'ila ke ci gaba da kai masu hari akai akai. 

An zana wannan zane-zanen a bangon tashar jiragen ruwa da nufin tunawa da rawar da mahalarta wannan jiragen ruwa suka taka da kuma yin Allah wadai da harin da gwamnatin Sahyoniya na ta kai musu a cikin ruwan ƙasa da ƙasa. Wannan aiki na alami yana nuna gwagwarmayar al'adu da fasaha na mutanen yankin Gaza game da killacewa da ci gaba da kai masu har

i.

Your Comment

You are replying to: .
captcha