Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): Hazrat Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, a cikin saƙonsa game da Ranar Ma'aikaci da Ranar Malami, yayin da yake yaba wa matsayi da darajarsu, ya jaddada muhimmancin cin nasara da rusa abokan gaba na ci gaba da martabar Iran a jihadin tattalin arziki da al'adu, kamar yadda yake a fagen yaƙin soja, kuma ya ɗauki malamai a matsayin mafi tasiri a yaƙin al'adu, kuma ma'aikata a matsayin mafi tasiri a yaƙin tattalin arziki kuma a matsayin kashin baya na fagen al'adu da tattalin arziki.
Wannan Shine Matanin Bayanin Na Sa:
Bismillahir Rahmanir Rahim
Kwanaki biyu sha ɗaya da sha biyu na watan Ordibehesht, su ne kwanakin da ake yaba wa martsayin ma'aikaci da darajar malami. Ba tare da la'akari da yabon baki da na alama ba, wanda shi kansa aiki ne da ya dace kuma daidai ne, ci gaban kowace ƙasa ya dogara ne da fikafikai biyu: ilimi da aiki. Malami yana taka rawa a matakin farko na cimma wannan manufa.
Nauyi mai girma na koyar da ilimi, haɓaka kwarewa, da wani muhimmin sashe na haɓaka mahanga da tsara asalin tsatso mai zuwa yana kan sa ne. Daliban makaranta, daliban jami'a, da ɗaliban addini waɗanda suke girma tare da kowane malami, ba da dadewa ba nan gaba, za su yi amfani da dabarun da suka koya da ilimin da suka koya, har ma ya zamo a halaye da ɗabi'a da maganganunsu a fannoni daban-daban, tun daga cikin dangi zuwa wurin aiki da lunguna da tituna, za su zama kamar madubi wajen nuna ɗabi'a da maganganun malamansu.
A gefe guda, fagen aiki fage ne mai faɗi gwargwadon ƙasar, wanda ya shimfiɗu tun daga cikin gidaje, ofisoshi, wuraren kasuwanci da masallatai, har zuwa gonaki, wuraren aiki, masana'antu, ma'adanai, da nau'ukan ayyukan hidima da dama. Yayin da wannan fage mai faɗi ya fi amfana da abubuwa biyu: aiki tuƙuru da sadaukarwa, waɗanda suke cikin ginshiƙan kowace nasara mai girma, to hakan yana ƙara tabbatar da ci gaban ƙasa da kyau.
Mun san cewa ma'aikaci, a cikin hasken sadaukarwa da kyakkyawan aiki, wani lokaci yana samun matsayi har ya cancanci a sumbaci hannunsa mai ƙarfi da fasaha don godiya da yabo, kamar yadda ake sumbatar hannun malami mai tausayi da mai tarbiyya. Wannan ba shakka abu ne da za a iya samu daga malaman farko na kowane mutum, wato iyayensa – mahaifinsa da mahaifiyarsa – sannan kuma daga fahimtar tarbiyyar malami.
Wanda Jamhuriyar Musulunci ta Iran, bayan fiye da shekaru arba'in da bakwai na gwagwarmaya, tare da dogaro ga falalar Allah, a yaƙin soja da abokan gaba na ci gabanta da martaba, ta tabbatar wa duniya wani ɓangare na iyawarta mai ban mamaki, to a mataki na jihadin tattalin arziki da al'adu ma dole ne ta yanke masu kauna ta kayar da su.
Malamai za su zama mafi tasiri a yaƙin al'adu, kuma ma'aikata za su kasance daga cikin mafi tasiri a yaƙin tattalin arziki; ta yadda za a iya da'awar cewa waɗannan biyu, kamar kashin baya ne na fagen al'adu da tattalin arziki.
Don haka ya zama dole su kasance da masaniya game da muhimmancin matsayinsu na musamman wanda ya wuce kawai zama wani aiki wanda ake karɓar albashi a kansa. Kamar yadda ma ya kamata a lura cewa, yin yabon baki na shekara-shekara ko lokaci-lokaci ko da yake ya dace kuma daidai ne, amma godiya ga ƙoƙarin waɗannan gungu biyu ya kamata ya fi zurfi kuma ya fi a aikace fiye da haka. Ni ina ganin kamar yadda al'ummar Iran masu daraja suka nuna goyon baya ga sojojin ƙasarsu ta hanyar halarta a filaye da tituna, ya kamata su nuna goyon baya mai ƙarfi a taimakon malamai da ma'aikata.
Daga cikin waɗannan, ya kamata a samar da mu'amalar iyalan ɗaliban makaranta da ɗaliban jami'a a cikin ma’aikatu da makarantu da jami'o'i fiye da yadda ake yi a da. Hakanan, ta hanyar ba da fifiko ga amfani da kayayyakin da aka kerawa a cikin ƙasa, a tallafa wa ma'aikata masu samarwa; kuma musamman masu kasuwancin da aka lalace, su guji rage ma'aikata da raba ma'aikatansu gwargwadon iko, ko a sassan samarwa ko sassan hidima, a maimakon haka su ɗauki kowane ma'aikaci a matsayin kadara ta wannan sashin kerawar da hidima. Kuma ba shakka gwamnati mai girma ta tallafa wa wannan aikin alheri gwargwadon ikonta.
Iran mai daraja, kamar yadda bayan shekaru na ƙoƙari ta bayyana a matsayin ƙarfin soja, in sha Allahu kuma da falalar Allah, ta hanyar zana layukan asalin Iran din Musulunci da shigar da shi sosai a cikin tunani da rayukan matasan wannan ƙasa ta hannun malamai da masu tarbiyya, da kuma ba da fifiko ga amfani da kayayyakin da aka kera a cikin ƙasa – wanda shine sakamakon ƙoƙarin ma'aikatan Iran masu aiki tuƙuru – za ta bi hanyar zuwa kololuwar ci gaba da martaba. Kuma wannan ba shakka, ta hanyar addu'a mai kyau da shiga tsakanin shugabanmu (Imamu Mahdi) – Allah ya gaggauta fitowarsa mai daraja – zai faru cikin sauri da inganci da iznin Allah.
Assalamu Alaikum Da Rahamar Allah Da Albarkarsa.
Sayyid Mujtaba Husayni Khamenei
11 Ordibehesht 1405 (1 Mayu 2026)
Your Comment