Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sa'a guda da ta gabata, sakamakon fashewar bam a titin Fatimiyya a yankin Zainabiyya na Damascus, limamin haramin tsarki na Sayyada Zainab (AS) Hujjatul-Islam "Sayyid Farhan Hassan Al-Mansur" ya yi shahada.
Kafin wannan, wasu rahotanni sun ba da labarin cewa "Sayyid Farhan Hassan Al-Mansur" ya ji rauni, amma cikakkun labarai sun nuna cewa wannan malamin Shi'a ya yi shahada.
Sayyid Farhan Hassan Al-Mansur, memba ne na majalisar malaman Shi'a na Syria kuma limamin haramin Sayyada Zainab (AS), wanda ya yi shahada saboda harin da aka kai masa.
…………………………………………..
Your Comment