9 Afirilu 2026 - 20:54
Source: ABNA24
Hizbullah: Zamu Ci Gaba Da Kai Wa Isra'ila Hari Har sai Ta Daina Harin Ta'addanci

Dangane da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da makiya ke yi bayan gwagwarmaya ta aiwatar da tsagaita wutar amma makiya ba su aiwatar da ita ba, mayakan gwagwarmayar Musulunci sun kai hari kan garin Al-Manara da makamai masu linzami. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wadannan martani za su ci gaba har sai an daina kai hare-hare a kasarmu da al'ummarmu.

Hizbullah na ci gaba Da Ruwan Makamai makami mai Linzami a yankunan da aka mamaye matsayin martani ga hare-haren da Isra'ila. A lokaci gudaan jiyo ƙararrawar gargadi a waɗannan wuraren.

Sannan Hizbullah ta fitar da bidiyon Yadda ta kai hari kan jirgin ruwan yakin Isra'ila a gabar tekun Lebanon da makamai masu linzami na ruwa.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha