9 Afirilu 2026 - 14:39
Source: ABNA24
Miliyoyin Al’ummar Iran Suka Gudanar Da Tarukan Juyayi Na Ciki 40 Da Shahadar Jagora Sayyid Ali Khamenei Qs

An kaddamar da jerin gwanon ta'aziyya na cika kwana arba'in shahadar shugaban al'umma, Imam Sayyid Khamenei (Allah ya yarda da shi) a Tehran da sauran biranen Iran.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Tehran a yau Alhamis, da karfe 9:40 na safe, miliyoyin al’umma suka fara tattakin juyayi daga dandalin Jamhuriyar Musulunci, zuwa wurin shahadar Sayyid Qa’id a ranar cika kwana 40 shahadar shugaban al'ummar Sayyid Imam Khamenei (Allah ya yarda da shi),

Kamar yadda aka tsara shirye-shiryen da aka sanar, an kaddamar da jerin gwanon jana'izar ne tun daga yammacin jiya Laraba, bayan sallar Magrib da Isha, daga masallatai da Husainiyoyi, zuwa kan matattarar manyan filaye da wurare masu tsarki a duk fadin kasar. A cikin wannan taron a yau Alhamis an yada addu'a Faraj ta Imam Zaman As da muryar jagoran al'umma a duk fadin kasar kuma an karanta addu’ar  a tare gaba daya.

Haka kuma za a gudanar da wannan taron a duk fadin kasar Iran a ranar Juma'a, wanda zai fara da karfe 10:00 na safe, a wuraren Sallar Juma'a a duk fadin kasar. An kuma kayyade karanta adadin Suratul Fathi miliyan biyu, da niyyar samun nasarar al'ummar Iran da kuma Fagen gwagwarmaya. Har ila yau, Iraniyawa za su gudanar da majalisun makoki a gidaje don tunawa da jagoranmu da ya yi shahada har zuwa gobe Juma'a

....................

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha