6 Afirilu 2026 - 22:14
Source: ABNA24
Amurka Da Isra'ila Sun Kai Hari Karo Na Hudu Cibiyar Makamashin Nukiliya Ta Bushehr

Kai hari kan cibiyar nukiliyar Bushehr shi ne shaida da ke tabbatar da laifukan yaƙi kuma rashin ɗaukar matakin hukumar Nukiliya shi ke sanya masu ta'addanci tsaurin kan kai hari.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A wata wasika da ya aike wa Rafael Grossi, Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta kasa da kasa (IAEA), shugaban kungiyar makamashin nukiliya ta Iran dangane da kai harin da Amurka da Isra'ila suka kai a rukunin 1 na tashar makamashin nukiliya ta Bushehr cewa a fili ya ke keta dokokin kasa da kasa ne da laifukan yaki kuma ya kira da hukumar ta gaggauta hukunta wannan ɗan yan aiki. 

Mohammad Eslami, mataimakin shugaban kasa kuma shugaban Ma'aikatar makamashin nukiliya, a wata wasika a hukumance da ya aike ta zuwa ga Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi, ya nuna rashin amincewarsa da harin da aka kai a baya bayan nan kan tashar makamashin nukiliyar Bushehr. Ya zo a cikin wannan wasikar; A safiyar ranar Asabar, 4 ga Afrilu, 2026, da misalin karfe 8:30 na agogon kasar, Iran ta fuskanci harin makamai masu linzami a kusa da shingen sashin farko na tashar makamashin nukiliya ta Bushehr (BNPP-1). Wani gini da ke cikin wurin ya lalace sakamakon fashewar da gutsuttsurun.makaman kuma daya daga cikin jami'an tsaro na tashar wutar lantarki yayi shahada tare da jikkata wasu da dama. 

Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada a wannan wasika; An kai wannan harin a karo na hudu a kan rukunin farko na tashar makamashin nukiliya ta Bushehr kuma zai iya haifar da haɗarin yaɗuwar sinadaran rediyo daga na'urar sarrafa kayan aiki; Batun da zai haifar da sakamako maras daɗi da ba za iya maganinsa ba ga jama'a, muhalli har ma da kasashe makwabta. 

Har ila yau, Iran ta Musulunci ta kira matakin a matsayin saba wa ka'idar hana kai hari kan cibiyoyin nukiliya a karkashin wata kasa memba na yarjejeniyar hana yaduwar makamashin nukiliya (NPT) tare da bayyana shi a matsayin misali karara na laifukan yaki da barazana ga tsarin duniya na hana yaduwarsa. 

A wani bangare na wannan wasika, an jaddada cewa; Wadannan hare-haren soji sun saba wa yarjejeniyar Geneva da ka'idoji, ka'idar IAEA, Yarjejeniyar Rashin Yaduwar Nukiliya (NPT), Yarjejeniyar Kariya ta Iran-IAEA (INFCIRC / 214), kwamitin gwamnoni, da ka'idojin aminci na IAEA. Shugaban kungiyar makamashin nukiliya ta Iran ya kuma soki rashin aikin hukumar da babban darakta a yayin da ake fuskantar wadannan hare-hare, inda ya bayyana cewa kawai bayyana nuna "damuwa mai zurfi" ba tare da la'akari da hukunta masu keta iyaka ba bai wadatar ba, kuma irin wannan hanyar na iya sa masu cin zarafi su ji tsaurin kan maimaita wadannan hare-haren. 

Wasikar ta kara da cewa: "A bayyane yake cewa wadannan rashin ɗaukar mataki akan ayyukan, musamman hirarraki da kalamai na siyasa na babban manajan, gami da abubuwan da ya faɗa a cikin hirar da cibiyar sadarwa ta CBS, sun sanya masu ta'addancin gwargwadon iko ci gaba da keta iyaka da rashin tausayi wanda ya saba wa ka'idoji da dokokin kasa da kasa. 

Babu shakka, ana ɗaukar ci gaba da waɗannan rashin hukuntawa a matsayin wani nau'i na haɗin gwiwa tare da masu laifi, kuma an rubuta wannan haɗin gwiwa a cikin tarihi har abada, kuma ba shakka, zai sa hukumar ta ƙara zama mara inganci. 

A cikin wannan wasika, mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da daraktan ta da su dauki kwararan matakai da yin yin Allah wadai da wadannan hare-hare kan cibiyoyin nukiliya a karkashin kariyar Iran tare da yin aiki da alhakin dokokinsu, ba wai kawai su zamo masu kallon lamarin ba. 

Islami ya jaddada a karshe; Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki matakan da suka dace don kare hakkinta. 

................

Your Comment

You are replying to: .
captcha