Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sansanin Khatamul-Anbiya, jaruman dakarun soji bisa goyon bayan jama'a sun fatattaki makiya Amurka da sahyoniyawan tare da lalata kayan aikinsu na yaki. Sa'a daya da ta gabata, jaruman sojojin da dakarun basij sun haifar da barna ga jiragen yakin Amurka wanda ya haifar da fatattakar abokan gaba da lalata kayan aikinsu. Kokarin da makiya ke yi ya ci tura bisa kulawar Allah Madaukakin Sarki da taimakonsa, inda aka aiwatar da ayyukan hadin gwiwa na mayakan Musulunci na rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci da sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da yin nasara da yin galaba a kan makiyiya Amurka inda Amurka ta gaza wajen ceto matuka jirginta da su ka fado. Sannan dakarun sun kakkabo jiragen abokan gaba a kudancin Isfahan, ciki har da jirage masu saukar ungulu na Black Hawk guda biyu da wani jirgin jigilar sojoji na C130. Bugu da ƙari, an lalata wasu kayan aiki daga abokan gaba, kuma za a fitar da ƙarin labarai dangane da haka.
Ofishin huldar jama'a na sojojin IRGC sun sanar da lalata jiragen sama guda biyu na abokan gaba nau’in MQ9 a sararin samaniyar Isfahan 'yan mintoci da suka gabata. Ofishin ya kuma sanar da lalata wani jirgin mara matuki na "Hermes 900" na maƙiya Amurka da sahyoniya ta hanyar harbin sa da tsarin tsaron sama na Sojoji a yankin Isfahan. Idan aka yi la’akari da wannan, adadin jirage marasa matuka da aka lalata ta hanyar haɗin gwiwar cibiyar tsaro ta haɗin gwiwa ta ƙasar ya kai 162.
Your Comment