2 Afirilu 2026 - 19:05
Source: ABNA24
Iran Ta Kama Sojojin Haya 810 Na Gwamnatin Isra’ila A Lardunan Hamedan, Lorestan Da Kerman Da Azerbaijan

Iran na ci gaba da ganowa da kama dukkan munafukai da masu hannu a bayar da bayanan sirri na ƙasar ga abokan gaba

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa:Ma'aikatar leken asiri ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran: 24 daga cikin wadannan jami’an sun aike da bayanan wuraren sojoji, jami'an tsaro da wuraren da suke aiki da kuma wurin ajiye kayan aikin soji suke a lardin Hamedan ga abokan gaba, kuma makiya Amurka da sahyoniyawa sun kai harin bam a da dama daga cikin wadannan wurare; an kama na’urorin Sterlink 11 a wadanna mutanen da wasu bindigogi manya da kanana.

An kuma gano tare da kama wasu sojojin haya hudu na wata kungiyar ta'addanci yayin da suke tattara bayanai ga jami'an leken asirin abokan gaba a lardin Lorestan. 'Yan ta'adda biyu sun kuma yi kokarin kwashe makamai a lardin Kerman bisa taimkon danginsu, amma da taimakon rahotannin jama'a sojojin Imam Zaman AF sun gano su tare da bindigu guda 7 da harsashi 10. Mai gabatar da kara Hamidiyeh: maha’inta biyu da ke da alaka da kungiyoyi da wasu ‘yan adawa a kasashen waje an gano su kuma sun kama su ta hanyar umarnin kotu. An tura wadanda ake tuhumar zuwa gidan yari tare da umarnin tsare su na wucin gadi don kammala binciken. Ya kara da cewa: Ba za mu yi saka-saka ga wadanda suka dauki wani mataki kan tsaron kasarmu ba kuma za a yi musu hukunci bisa ka'ida.

Babban kwamandan kasar: Tun farkon yakin Ramadan, an kama mambobi 48 daga cikin manyan masu hatsari da suke kiyayya da juyin juya hali da ayyukan leken asiri. Tare da matakan leken asirin 'yan sanda, an kama mutne 46 da suke hulda da sayar da nau’rar Starlink a larduna 19 an gano su kuma an kama su bayan gano na'urorin Starlink 139 da masu amfani da hanyoyin sadarwa.

Baya ga kama mutane 77 marasa kishin kasa da masu kwadayin mulki da yan korensu a kafofin sadarwa; an kama Maha’inta 97 Masu aikata laifuka da masu cin amana wadanda ke ci gaba da hada kai da cibiyoyin yada labarai na ta'addanci masu alaka da ayyukan leken asirin abokan gaba ta hanyar aika hotunan wurin makami mai linzami. Sannan an kuma gano tare da kama mutane 481 da suka kawo cikas da rudani ga tsaron tunanin al'umma a kafofin sadarwa.

Dangane da ayyukan da rahotannin jama'a, IRGC ta gano tare da kama jami’ai da ke leken asirin tsaro a lardin Tsakiya. Daya daga cikin su ya kasance ɗan leƙen asiri ne a ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin larduna waɗanda, yayin da suke tattara bayanai na musamman don tuntuɓar jami'in leken asiri na gwamnatin sahyoniya, sun yi niyyar aika bayanai da zagon ƙasa, amma sun gaza har aka kama su.

An kama wasu mutane 65 da ke da alaka da Isra'ila Jami’an Leken Asiri ta Lardin IRGC ta Tsakiya: an gano da kama wani mutum ɗaya shi ma da aiki a cikin manyan cibiyoyin lardin yayin da yake tattara bayanai na musamman don aikawa ga jami'in leken asiri na gwamnatin sahyoniyawa.

Sannan an cafke mambobi takwas daga cikin kungiyoyin ta'addanci bayan binciken bayanan sirri a yammacin lardin Azerbaijan. An kuma gano babba motar jigilar kayan aikin sadarwa na leƙen asiri na abokan gaba a kan iyakokin arewa maso yamma. Kayayyakin sun hada da na'urorin sadarwa na zamani guda 45 da aka shirya don leken asiri da tattara bayanan Iran.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha